1
Suna tambayar ka ga ganĩma. ka ce: "Ganĩma ta Allah daManzonSa ce. Sai ku bi Allah da taƙawa, kuma ku gyãra abin da yake a tsakãninku, kuma ku yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, idan kun kasance mũminai."
2
Abin sani kawai, nũminai sũ ne waɗanda suke idan an ambaci, Allah, zukãtansu su firgita, kuma idan an karanta ãyõyinSa a kansu, su ƙãrã musu wani ĩmãni, kuma ga Ubangijinsu suke dõgara.
3
Waɗanda suke tsayar da salla, kuma daga abin da Muka azũrtã su sunã ciyarwa.
4
Waɗannan sũ ne mũminai da gaskiya. Sunã da darajõji a wurin Ubangijinsu, da wata gãfara da arziki na karimci.
5
Kamar yadda Ubangijinka Ya fitar da kai daga gidanka da gaskiya, alhãli kuwa lalle wani ɓangare na mũminai, haƙĩƙa, sunã ƙyãma.
6
Sunã jãyayya da kai a cikin (sha'anin) gaskiya a bãyan tã bayYanã, kamar dai lalle anã kõra su zuwa ga mutuwa ne alhãli kuwa sunã kallo.
7
Kuma a lõkacin da Allah Yake yi muku alkawari da ɗayan ƙungiya biyu, cẽwa lalle ita tãku ce: kuma kunã gũrin cẽwa lalle ƙungiya wadda bã ta da ƙaya ta kasance gare ku, kuma Allah Yanã nufin Ya tabbatar da gaskiya da kalmõminSa, kuma Ya kãtse ƙarshen kãfirai;
8
Dõmin Ya tabbatar da gaskiya, kuma Ya ɓãta ƙarya, kuma kõdã mãsu laifi sun ƙi.
9
A lõkacin da kuke nẽman Ubangijinku tairnako, sai Ya karɓa muku cẽwa: "Lalle ne Nĩ, Mai taimakon ku ne da dubu daga malã'iku, jẽre."
10
Kuma Allah bai sanya shi ba fãce Dõmin bishãra, kuma dõmin zukãtanku su natsu da shi, kuma taimakon, bai zama ba fãce daga wurin Allah; Lalle ne Allah Mabuwãyi ne, Mai hikima.
11
A lõkacin da (Allah) Yake rufe ku da gyangyaɗi, ɗõmin aminci daga gare Shi, kuma Yanã saukar da ruwa daga sama, a kanku, dõmin Ya tsarkake ku da shi, kuma Ya tafiyar da ƙazantar Shaiɗan daga barinku, kuma dõmin Ya ɗaure a kan zukãtanku, kuma Ya tabbatar da ƙafãfu da shi.
12
A lõkacin da Ubangijinka Yake yin wahayi zuwa ga Malã'iku cẽwa: "Lalle ne Ni, Inã tãre da ku, sai ku tabbatar da waɗanda suka yi ĩmãni: Zã Ni jẽfa tsõro a cikin zukãtan waɗanda suka kãfirta, sai ku yi dũka bisa ga wuyõyi kuma ku yi dũka daga gare su ga dukkan yãtsu.
13
Wancan ne, dõmin lalle ne sũ, sunã sãɓa wa Allah da ManzonSa. Kuma wanda ya sãɓa wa Allah da ManzonSa, to, lalle ne Allah Mai tsananin uƙũba ne.
14
Wancan ne: "Ku ɗanɗane shi, kuma lalle ne akwai azãbar wuta ga kãfirai."
15
Yã kũ wacɗanda suka yiĩmãni! Idan kun haɗu da waɗanda suka kãfirta ga yãƙi, to, kada ku jũya musu bãyayyakinku.
16
Kuma duka wanda ya jũya musu bãyansa a yinin nan, fãce wanda ya karkata dõmin kõɗayya, kõ kuwa wanda ya jẽ dõmin haɗuwa da wata ƙungiya, to, lalle ne ya kõma da fushi daga Allah, kuma matattararsa Jahannama, kuma tir da makõma ita!
17
To, bã kũ ne kuka kashe su ba; kuma amma Allah ne Ya kashe su: kuma ba ka yi jĩfa ba a lõkacin da ka yi jĩfa; kuma amma Allah ne Ya yi jĩfar. Kuma dõminYa jarraba Musulmi da jarrabãwa mai kyau daga gare shi. Kuma Allah Mai ji ne, Masani.
18
Wancan ne, kuma lalle ne, Allah Mai raunana kaidin kãfirai ne.
19
Idan kun yi alfãnun cin nasara to lalle nasarar tã je muku, kuma idan kun hanu, to Shi ne Mafi alhẽri a gare ku, kuma idan kun kõma zã Mu kõma, kuma jama'arku bã zã ta wadãtar muku da kõme ba, kõ dã tã yi yawa. Kuma lalle ne cẽwa Allah Yanã tãre da mũminai!
20
Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, kuma kada ku jũya daga barinSa, alhãli kunã ji.
21
Kuma kada ku kasance kamar waɗanda suka ce: "Mun ji, alhãli kuwa sũ bã su ji."
22
Lalle ne, mafi sharrin dabbõbi a wurin Allah, sũ ne kurãme, bẽbãye, waɗanda bã, su yin hankali.
23
Dã Allah Yã san wani alhẽri a cikinsu, dã Yã jiyar da su, kuma kõ da Yãjiyar da su, haƙĩƙa, dã sun jũya, alhãli sũ, sunã mãsu hinjirẽwa.
24
Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku karɓa wa Allah, kuma ku karɓa wa Manzo, idan Ya kirãye ku zuwa ga abin da Yake rãyar da ku; Kuma ku sani cẽwa Allah Yanã shãmakacẽwa a tsakãnin mutum da zũciyarsa, kuma lalle ne Shĩ, a zuwa gare Shi ake tãra ku.
25
Kuma ku ji tsõron fitina wadda bã ta sãmun waɗanda suka yi zãlunci daga gare ku kẽɓe, kuma ku sani, lalle ne Allah Mai tsananin uƙũba ne.
26
Ku tuna a lõkacin da kuke kaɗan, waɗanda ake raunanarwã a cikin ƙasa kunã tsõron mutãne su cafe ku, sai Ya tattara ku (a wurin natsuwa, Maɗina), kuma Ya ƙarfafã ku da taimakonSa kuma Ya azurtã ku daga abũbuwa mãsu dãɗi; Tsammãninku, kunã gõdẽwa.
27
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku yaudari Allah da ManzonSa, kuma ku yaudari amãnõninku, alhãli kuwa kunã sane.
28
Kuma ku sani cẽwa abin sani kawai, dũkiyõyinku da 'ya'yanku, wata fitina ce, kuma lalle ne Allah, a wurinSa, akwai ijãra mai girma.
29
Ya kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan kun bi Allah da taƙawa, zai sanyã muku mararraba (da tsõro) kuma Ya kankare ƙanãnan zunubanku daga barinku. Kuma Ya gãfartã muku. Kuma Allah ne Ma'abũcin falalã Mai girma.
30
Kuma a lõkacin da waɗanda suka kãfirta sukẽ yin mãkirci game da kai, dõmin su tabbatar da kai, kõ kuwa su kashe ka, kõ kuwa su fitar da kai, sunã mãkirci kuma Allah Yanã mayar musa da mãkirci kuma Allah ne Mafificin mãsu mãkirci.
Sonraki 30 ayet →