Ana SayfaMealler › M.Gumi
MG

M.Gumi

M.Gumi
M.Gumi meali ile okumaya başla
Nuh 1 / 28
1
Lalle ne Mun aiki Nũhu zuwa ga mutãnensa, cẽwa ka yi gargaɗi ga mutãnenka gabãnin wata azãba mai raɗaɗi ta zo musu.
M.Gumi 71:1
2
Ya ce: "Ya mutãnena ni, a gare ku, mai gargaɗi ne, mai bayyanãwa."
M.Gumi 71:2
3
Cewa ku bauta wa Allah, ku ji tsõronSa, kuma ku bĩ ni.
M.Gumi 71:3
4
Allah zai gãfarta muku daga zunubanku kuma Ya jinkirta muku zuwa ga ajalin da aka ambata. Lalle ne ajalin Allah idan ya zo, ba za a jinkirta Shi ba, dã kun kasance masana (ga abin da nake faɗã dã, kun bar kãfirci).
M.Gumi 71:4
5
Nũhu) ya ce: "Ya Ubangijina! Lalle ne, na kirãyi mutãnena, a cikin dare da yini."
M.Gumi 71:5
6
To, amma kirana bai ƙãre su ba sai da, gudu (daga gare ni).
M.Gumi 71:6
7
Kuma lalle ne ni, kõ da yaushe na kirãye su dõmin Ka gãfarta musu, sai su sanya yatsunsu a cikin kunnuwansu, su lulluɓe da tufãfinsu, su dõge ga yin laifi. Sun yi girman kai iyãkar girman kai.
M.Gumi 71:7
8
Sa'an nan lalle ne ni, na kira su, a bayyane.
M.Gumi 71:8
9
Sa'an nan lalle ne, na yi yẽkuwa sabõda su, kuma na gãna da su a cikin asĩri.
M.Gumi 71:9
10
Shi na ce, 'Ku nẽmi gãfara daga Ubangijinku, lalle ne shi Ya kasance Mai gãfara ne.
M.Gumi 71:10
11
Ya sako (girgijen) sama a kanku da ruwa mai ɓuɓɓuga.
M.Gumi 71:11
12
Kuma ya yalwata muku game da dũkiya da ɗiya, Ya sanya muku (albarka) ga gõnaki, kuma Ya sanya muku koguna.
M.Gumi 71:12
13
Me ya sãme ku, bã ku fãtar sãmun natsuwa daga Allah,
M.Gumi 71:13
14
Alhãli kuwa, lalle ne, Ya halitta. ku, a cikin hãlãye?
M.Gumi 71:14
15
Ba ku ga yadda Allah Ya halitta wasu sammai bakwai ɗabaƙõƙĩ a kan jũna ba?
M.Gumi 71:15
16
Ya sanya watã a cikinsu, yana mai haske, Ya sanya rãnã babbar fitila?
M.Gumi 71:16
17
Kuma Allah Ya tsirar da ku daga ƙasa (kamar ganye) tsirarwa.
M.Gumi 71:17
18
Sa'an nan Ya mayar da ku a cikinta, kuma Ya fitar da ku fitarwa.
M.Gumi 71:18
19
Kuma Allah Ya sanya muku ƙasa shimfidaɗɗiya.
M.Gumi 71:19
20
Dõmin ku shiga a cikinta, hanyõyi mãsu fãɗi.
M.Gumi 71:20
21
Nũhu ya ce: "Ya Ubangijina! Lalle ne sũ sun saɓa mini sun bi wanda dukiyarsa da ɗiyansa ba su ƙãre shi da kõme ba sai da hasãra."
M.Gumi 71:21
22
Kuma sun yi wani mãkirci, mãkirci babba.
M.Gumi 71:22
23
Kuma suka ce: Faufau kada ku bar gumãkanku, kuma faufau, kada ku bar wadda, kuma kada ku bar suwã kuma kada ku bar Yagũsa da Ya'ũƙa da Nasra.
M.Gumi 71:23
24
Kuma lalle ne sun ɓatar da (mutãne) mãsu yawa, kuma kada Ka ƙãrã wa azzãlumai (kõme) sai ɓata.
M.Gumi 71:24
25
Sabõda laifukansu na ganganci aka nutsar da su, sa'an nan aka sanya su a wuta. Saboda haka ba su sãmã wa kansu wani mataimaki wanin Allah ba.
M.Gumi 71:25
26
Kuma Nũhu ya ce: "Ya Ublngijina! Kada Ka bari, a kan ƙasa, daga cikin kãfirai, wanda ke zama a cikin gida."
M.Gumi 71:26
27
Lalle ne, Kai idan Ka bar su, zã su ɓatar da bãyinKa, kuma bã zã su haifi kowa ba fãce fãjiri mai yawan kãfirci
M.Gumi 71:27
28
Ya Ubanginjina! Ka yi mini gãfara (ni) da mahaifana biyu, da wanda ya shiga gidana, yana mai ĩmãni, da mũminai maza da mũminai mãtã, kuma kada Ka ƙãrã wa azzãlumai kõme sai halaka.
M.Gumi 71:28
Nuh suresi tamamlandı