Ana SayfaMealler › M.Gumi
MG

M.Gumi

M.Gumi
M.Gumi meali ile okumaya başla
Necm 1 / 62
1
Inã rantsuwa da taurãron, a lõkacin da ya faku.
M.Gumi 53:1
2
Ma'abũcinku bai ɓata ba, kuma bai ƙẽtare haddi ba.
M.Gumi 53:2
3
Kuma bã ya yin magana daga son zuciyarsa.
M.Gumi 53:3
4
(Maganarsa) ba ta zamo ba, fãce wahayi ne da ake aikõwa.
M.Gumi 53:4
5
(Malã'ika) mai tsananin ƙarfi ya sanar da shi.
M.Gumi 53:5
6
Ma'abũcin ƙarfi da kwarjini, sa'an nan ya daidaita.
M.Gumi 53:6
7
Alhãli kuwa yanã a sararin samã mafi aukaka.
M.Gumi 53:7
8
Sa'an nan ya kusanta, kuma ya matsa zurõwa.
M.Gumi 53:8
9
Har ya kasance gwargwadon zirã'i biyu, kõ kuma abin da ya fi kusa.
M.Gumi 53:9
10
Sa'an nan ya yi wahayi zuwa ga bãwan Allah (Muhammadu) da abin da ya faɗa (masa).
M.Gumi 53:10
11
Zũciyar (Annabi) bata ƙaryata abin da ya gani ba.
M.Gumi 53:11
12
Shin, zã ku yi masa musu a kan abin da yake gani?
M.Gumi 53:12
13
Kuma lalle ya gan shi, haƙĩƙatan, a wani lõkacin saukarsa.
M.Gumi 53:13
14
A wurin da magaryar tuƙẽwa take.
M.Gumi 53:14
15
A inda taken, nan Aljannar makoma take.
M.Gumi 53:15
16
Lõkacin da abin da yake rufe magaryar tuƙẽwa ya rufe ta.
M.Gumi 53:16
17
Ganinsa bai karkata ba, kuma bai ƙetare haddi ba.
M.Gumi 53:17
18
Lalle, tabbas, (Annabinku) ya ga waɗanda suka fi girma daga ãyõyin Ubangijinsa.
M.Gumi 53:18
19
Shin, kun ga Lãta da uzza?
M.Gumi 53:19
20
Da (wani gunki wai shi) Manãta, na ukunsu?
M.Gumi 53:20
21
Ashe, kũ ne da ɗa namiji Shĩ (Allah) kuma da ɗiya mace?
M.Gumi 53:21
22
Wannan fa ya zama rabo naƙasasshe.
M.Gumi 53:22
23
Waɗannan bã kõme ba ne fãce sũnãye, waɗanda kuka ambace su da su, kũ da uwãyenku. Allah bai saukar da wani dalĩli game da su ba. (Kãfirai) bã su biyar kõme fãce zato da abin da rãyukansu ke so, Alhãli kuwa shiriyar ta daga wajen Ubangijinsu, ta jẽ musu (sai suka bar ta suka kõma wa zaton).
M.Gumi 53:23
24
Ko (an fai cẽwa) mutum zai sãmi abin da yake gũri?
M.Gumi 53:24
25
To, Lãhira da dũniya na Allah kawai ne (wanda ya nẽme su daga wani, yã yi kuskure).
M.Gumi 53:25
26
Akwai malã'iku da yawa a cikin sammai cẽtonsu bã ya wadãtar da kõme fãce bãyan Allah Yã yi izni (da shi) ga wanda Yake so, kuma Yake yarda.
M.Gumi 53:26
27
Lalle waɗannan da bã su yin ĩmãni da Lãhira, haƙĩƙa sunã kiran malã'iku da sũnan mace.
M.Gumi 53:27
28
Kuma bã su da wani ilmi game da shi, bã su bin kõme fãce zato alhãli kuwa lalle zato bã ya amfãnar da kõme daga gaskiya.
M.Gumi 53:28
29
Sabõda haka sai ka kau da kai daga wanda ya jũya bãya daga ambatonMu kuma bai yi nufin kõme ba fãce rãyuwar kusa (dũniya).
M.Gumi 53:29
30
Wannan ita ce iyãkar abin da suke iya kai gare shi na ilmi. lalle Ubangijinka Shĩ ne Mafi sanin wanda ya ɓace daga hanyarSa, kuma Shi ne Mafi sani ga wanda ya nẽmi shiriya.
M.Gumi 53:30