Ana SayfaMealler › M.Gumi
MG

M.Gumi

M.Gumi
M.Gumi meali ile okumaya başla
Tur 1 / 49
1
Inã rantsuwa da ¦ũr (Dũtsen Mũsã).
M.Gumi 52:1
2
Da wani littãfi rubũtacce.
M.Gumi 52:2
3
A cikin wata takardar fãta shimfiɗaɗɗa.
M.Gumi 52:3
4
Da Gidan da aka rãyar da shi (da ibãda).
M.Gumi 52:4
5
Da rufin nan da aka ɗaukaka.
M.Gumi 52:5
6
Da tẽkun nan da aka cika (da ruwa).
M.Gumi 52:6
7
Lalle, azãbar Ubangijinka, haƙĩƙa, mai aukuwa ce.
M.Gumi 52:7
8
Bã ta da mai tunkuɗẽwa.
M.Gumi 52:8
9
Rãnar da samã ke yin mõtsi tanã kai kãwo.
M.Gumi 52:9
10
Kuma duwãtsu nã tafiya sunã shũɗẽwa.
M.Gumi 52:10
11
To, bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa.
M.Gumi 52:11
12
Waɗanda suke a cikin kududdufi sunã wãsã.
M.Gumi 52:12
13
Rãnar da zã a tunkuɗa su zuwa wutar Jahannama, tunkuɗãwa.
M.Gumi 52:13
14
(A ce musu): "Wannan ita ce wutar da kuka kasance kunã ƙaryatãwa game da ita."
M.Gumi 52:14
15
To, shin wannan sihiri ne kõ kuwa kũ ne bã ku gani?
M.Gumi 52:15
16
Ku shigẽ ta. To, ku yi haƙuri ko kuma kada ku yi haƙuri, dai dai ne a kanku, kawai anã yi muku sakamakon abin da kuka kasance kunã aikatãwa.
M.Gumi 52:16
17
Lalle, mãsu taƙawa, sunã a cikin gidãjen Aljanna da wata ni'ima.
M.Gumi 52:17
18
Sunã mãsu jin dãɗi da abin da Ubangijinsu Ya ba su, kuma Ubangijinsu Ya tsãre musu azãbar Jahĩm.
M.Gumi 52:18
19
(A ce musu): "Ku ci, ku sha, da ni'ima, dõmin abin da kuka kasance kunã aikatãwa."
M.Gumi 52:19
20
Sunã kishingiɗe a kan karagu waɗanda ke cikin sahu, kuma Muka aurar da su waɗansu mãtã mãsu farin idãnu, mãsu girmansu.
M.Gumi 52:20
21
Kuma waɗanda suka yi ĩmãni kuma zũriyarsu suka bĩ su ga ĩmãnin, Mun riskar da zũriyarsu da su, alhãli kuwa bã da Mun rage musu kõme ba daga aikinsu, kõwane mutum jingina ne ga abin da ya sana'anta.
M.Gumi 52:21
22
Kuma Muka yalwata musu 'ya'yan itãce da nãma irin wanda suke marmari.
M.Gumi 52:22
23
Sunã mĩƙa wa jũnansu a cikinta hinjãlan giya, wadda bãbu yãsassar magana a cikinta, kuma bãbu jin nauyin zunubi.
M.Gumi 52:23
24
Kuma waɗansu samãri nã gẽwayãwa a kansu, kamar dai sũ lu'ulu'u ne wanda ke kulle.
M.Gumi 52:24
25
Waɗansunsu suka fuskanta zuwa ga waɗansu, sunã tambayar jũna.
M.Gumi 52:25
26
Suka ce: "Lalle mũ mun kasance a gabãnin wannan (a dũniya) a cikin iyãlanmu munã jin tsõro."
M.Gumi 52:26
27
To, Allah Yã yi mana kyautar falala, kuma Yã tsare mana azãbar iskar zãfi.
M.Gumi 52:27
28
Lalle mũ mun kasance, a gãbanin haka, munã kiran sa. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai kyautatãwa, Mai rahama.
M.Gumi 52:28
29
To, ka tunãtar kai fa sabõda ni'imar Ubangjinka, bã bõka kake ba, kuma bã mahaukaci ba.
M.Gumi 52:29
30
Shin zã su ce: "Mawãƙi ne, munã jiran, masĩfun mutuwa game da shĩ"?
M.Gumi 52:30