Ana SayfaMealler › M.Gumi
MG

M.Gumi

M.Gumi
M.Gumi meali ile okumaya başla
Duhan 1 / 59
1
Ḥ. M̃.
M.Gumi 44:1
2
Inã rantsuwa da Littãfi Mabayyani.
M.Gumi 44:2
3
Lalle ne, Mũ, Muka saukar da shi a cikin wani dare mai albarka. Lalle Mũ' Mun kasance Mãsu yin gargaɗi.
M.Gumi 44:3
4
A cikinsa (shi daren) ake rarrabe kõwane umurui bayyananne.
M.Gumi 44:4
5
Umurni na daga wurinMu. Lalle Mũ ne Muka kasanceMãsu aikãwã.
M.Gumi 44:5
6
Sabõda rahama daga Ubangijinka. Lalle Shĩ, Shi ne Mai ji, Mãsani.
M.Gumi 44:6
7
(Shĩ ne) Ubangijin sammai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu, idan kun kasance mãsu yaƙĩni (za ku gãne haka).
M.Gumi 44:7
8
Babu abin bautãwa fãce Shi. Yana rãyarwa Kuma Yana kashẽwa. (Shi ne) Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku na farko.
M.Gumi 44:8
9
A'a sũ, sunã wãsã a cikin shakka.
M.Gumi 44:9
10
Sabõda haka, ka dakata rãnar da sama zã tã zo da hayãƙi bayyananne.
M.Gumi 44:10
11
Yanã rufe mutãne. Wannan wata azãba ce mai raɗaɗi.
M.Gumi 44:11
12
Ya Ubangijinmu! Ka kuranye mana azãba. Lalle Mũ, mãsu ĩmãni ne.
M.Gumi 44:12
13
Inã tunãwa take a gare su, alhãli kuwa, haƙĩƙa, Manzo mai bayyanãwa Ya je musu (da gargaɗin saukar azãbar, ba su karɓa ba)?
M.Gumi 44:13
14
Sa'an nan suka jũya baya daga gare shi, Kuma suka ce: "Wanda ake gayãwa ne, mahaukaci."
M.Gumi 44:14
15
Lalle Mũ, Mãsu kuranyẽwar azãba ne, a ɗan lõkaci kaɗan, lalle kũ, mãsu kõmãwa ne (ga laifin).
M.Gumi 44:15
16
Rãnar da Muke damƙa, damƙa mafi girma, lalle ne Mũ mãsu azãbar rãmuwa ne.
M.Gumi 44:16
17
Kuma lalle ne haƙĩƙa a gabaninsu, Mun fitini mutãnen Fir'auna, kuma wani Manzo karĩmi ya jẽ musu.
M.Gumi 44:17
18
(Mazon ya ce): "Ku kãwo mini (ĩmãninku) ya bayin Allah! Lalle ni, Manzo ne amintacce zuwa gare ku."
M.Gumi 44:18
19
Kuma kada ku nẽmi ɗaukaka a kan Allah. Lalle nĩ mai zo muku ne da dalĩli bayyananne.
M.Gumi 44:19
20
Kuma lalle nĩ na nẽmi tsari da Ubangijĩna, kuma Ubangijinku, dõmin kada ku jẽfe ni.
M.Gumi 44:20
21
Kuma idan ba ku yi ĩmãni sabõda nĩ ba, to, ku nĩsance ni.
M.Gumi 44:21
22
Sai ya kirayi Ubangjinsa cẽwa waɗannan mutãnene mãsu laifi.
M.Gumi 44:22
23
(Allah Ya ce): "To, ka yi tafiyar dare da bayiNa, da dare. Lalle kũ, waɗanda ake bĩ ne (dõmin a kãma ku.)"
M.Gumi 44:23
24
Kuma ka bar tẽku rarrabe. Lalle sũ, runduna ce abar nutsarwa.
M.Gumi 44:24
25
Da yawa suka bar gõnaki da marẽmari.
M.Gumi 44:25
26
Da shuke-shuke da matsayi mai kyau.
M.Gumi 44:26
27
Da wata ni'ima da suka kasance a cikinta sunã mãsu hutu.
M.Gumi 44:27
28
Kamar haka! Kuma Muka gãdar da ita ga waɗansu mutãne na dabam.
M.Gumi 44:28
29
Sa'an nan samã da ƙasã ba su yi kũka a kansu ba, Kuma ba su kasance waɗanda ake yi wa jinkiri ba.
M.Gumi 44:29
30
Kuma lalle ne, haƙĩƙa Mun tsĩrar da Banĩ Isrã'ĩla daga, azãba mai wulãkantãwa.
M.Gumi 44:30