2
Saukar da Littãfi daga Allah ne, Mabuwãyi, Masani.
3
Mai gãfarta zunubi kuma Mai karɓar tũba Mai tsananin azãba, Mai wadãtarwa bãbu abin bautawa fãce Shi, zuwa gare Shi makõma take.
4
Bãbu mai jãyayya a cikin ãyõyin Allah, fãce waɗanda suka kãfirta. Sabõda haka kada jũyãwarsu a cikin garũruwa ta rũɗe ka
5
Mutãnen Nũhu sun ƙaryata a gabãninsu, da ƙungiyõyin da suke a bãyansu, kuma kõwace al'umma tã yi nufi game da Manzonsu, dõmin su kãmã shi. Kuma suka yi jãyayya da ƙarya dõmin su gusar da gaskiya da ita. Sai Na kãmã su. To, yãya azãbãTa take?
6
Kuma kamar haka kalmar Ubangijinka ta wajaba a kan waɗanda suka kãfirta, dõmin sũ 'yan wutã ne.
7
Waɗanda ke ɗaukar Al'arshi da waɗanda ke kẽwayenta, sunã tasbĩhi game da gõde wa Ubangijinsu, kuma sunã yin ĩmãni da Shi, kuma sunã yin istigfãri dõmin waɗanda suka yi ĩmãni, (sunã cẽwa), "Yã Ubangijinmu! Kã yalwaci dukan kõme da rahama da ilmi to Ka yi gãfara ga waɗanda suka tũba kuma suka bi hanyarKa, kuma Ka tsare musu azãbar Jahĩm."
8
Ya Ubangijinmu! Kuma Ka shigar da su a gidãjen Aljannar zama, wannan da Ka yi musu wa'adi, sũ da wanda ya kyautatu daga ubanninsu da mãtan aurensu da zurriyarsu. Lalle Kai, Kai ne Mabuwãyi, Mai hikima.
9
Kuma Ka tsare su daga mũnãnan ayyuka, kuma wanda Ka tsare shi daga mũnãnan ayyuka a rãnarnan, to, lalle, Ka yi masa rahama kuma wancan shi ne babban rabo mai girma.
10
Lalle waɗanda suka kãfirta, anã kiran su, "Haƙĩƙa, ƙin Allah (a gare ku) shĩ ne mafi girma daga ƙinku ga kanku a lõkacin da ake kiran ku zuwa ga ĩmãni, sai kunã ta kãfircẽwa."
11
Suka ce: "Ya Ubangijinmu! Kã matar da mu sau biyu, kuma Kã rãyar da mu sau biyu, sabõda haka mun yarda da laifuffukan mu. To, shin, akwai wata hanya zuwa ga fita?"
12
Wancan sababinsa, lalle (shi ne) idan an kirãyi Allah Shi kaɗai, sai ku kãfirta, kuma idan aka yi shirki game da Shi, sai ku yi ĩmãni. To, hukuncin fa, na Allah Maɗaukaki, Mai girma ne.
13
Shĩ ne Wanda ke nũna muku ãyõyinSa, kuma Ya saukar da arziki daga sama sabõda ku, kuma bãbu mai yin tunãni fãce mai mayar da al'amari ga Allah.
14
Sabõda haka ku kirãyi Allah, kunã mãsu tsarkake addini a gare Shi, kuma kõ dã kãfirai sun ƙi.
15
Mai ɗaukaka darajõji (dõmin mũminai), Mai Al'arshi, Yanã jẽfa rũhi daga al'amarinSa a kan wanda Ya so daga bãyinSa, dõmin ya yi gargaɗi kan rãnar gamuwa.
16
Rãnar da suke bayyanannu, bãbu wani abu daga gare su wanda yake iya bõyuwa ga Allah. "Mulki ga wa ya ke a yau?" Yana ga Allah, Makaɗaici, Mai tĩlastãwa.
17
Yau anã sãka wa kõwane rai a game da abin da ya aikata, bãbu zãlunci a yau. Lalle Allah Mai gaggawar hisãbi ne.
18
Kuma ka yi musu gargaɗi kan rãnar (Sã'a) makusanciya, a lõkacin da zukãta suke mãsu cika da bakin ciki, ga maƙõsansu. Bãbu wani masõyi ga azzãlumai, kuma bãbu wani mai cẽto da zã a yi wa dã'a (ga cẽtonsu).
19
(Allah) Ya san yaudarar idãnu da abin da ƙirãza ke ɓõyẽwa.
20
Kuma Allah Shĩ ke yin hukunci da gaskiya, waɗannan da kuke kira, waninSa, bã su yin hukunci da kõme. Lalle Allah, Shĩ ne Mai ji, Mai gani.
21
Ashe, ba su yi tafiya ba, a cikin ƙasã, dõmin su dũba ga yadda ãƙibar waɗanda suka kasance a gabãninsu ta zama? Sun kasance sũ ne mafi tsananin ƙarfi daga gare su, da kufaifan aiki a cikin ƙasã, sai Allah Ya kãmã su da laifuffukansu. Kuma bã su da wani mai tsarẽwa daga Allah.
22
Wancan sababinsa, dõmin sũ Manzanninsu sun kasance sunã zuwa gare su da hujjõji bayyanannu, sai suka kãfirta, sai Allah Ya kãmã su. Lalle Shĩ Mai ƙarfi ne, Mai tsananin azãba.
23
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika Mũsã a game da ãyõyinMu da wani dalĩli bayyananne.
24
Zuwa ga Fir'auna da Hãmãna da Kãrũna, sai suka ce: "Mai sihiri ne, maƙaryaci."
25
Sa'an nan, a lõkacin da ya jẽ musu da gaskiya daga wurinMu, suka ce: "Ku kashe ɗiyan waɗanda suka yi ĩmãni tãre da shi, kuma ku rãyar da mãtansu." Kuma mugun shirin kãfirai, bai zama ba fãce a cikin bata.
26
Kuma Fir'auna ya ce: "Ku bar ni in kashe Mũsã, kuma shĩ, ya kirãyi Ubangijinsa. Lalle ne nĩ, inã tsõron ya musanya addininku, kõ kuwa ya bayyana ɓarna a cikin kasã."
27
Kuma Mũsã ya ce: "Lalle nĩ, nã nẽmi tsari da Ubangijĩna kuma Ubangijinku, daga dukan makangari, wanda bã ya ĩmani da rãnar Hisãbi."
28
Kuma wani namiji mũmini daga dangin Fir'auna, yanã bõye ĩmãninsa, ya ce: "Ashe, za ku kashe mutum dõmin ya ce Ubangijina Allah ne, alhãli kuwa haƙĩƙa ya zo muku da hujjõji bayyanannu daga Ubangijinku? Idan yã kasance maƙaryaci ne, to, ƙaryarsa na kansa, kuma idan ya kasance mai gaskiya ne, sãshen abin da yake yi muku wa'adi zai sãme ku. Lalle ne Allah bã Ya shiryar da wanda yake mai barna, mai yawan ƙarya."
29
Yã kũ mutãnẽna! Kunã da mulki a yau, kuma kũ ne marinjãya a cikin kasã to wãne ne zai taimake mu daga azãbar Allah idan ta zo mana? Fir'auna ya ce: "Bã ni nũnamuku kõme face abin da na gani, kuma ba ni shiryar da ku, sai ga hanyar shiryuwa."
30
Kuma wannan da ya yi ĩmãni ya ce: "Ya mutãnẽnã! Lallene, nĩ, inã yi muku tsõron kwatankwacin rãnar ƙungiyõyi."
Sonraki 30 ayet →