Ana SayfaMealler › M.Gumi
MG

M.Gumi

M.Gumi
M.Gumi meali ile okumaya başla
Zümer 1 / 75
1
Saukar da Littãfin daga Allah ne, Mabuwãyi, Mai hikima.
M.Gumi 39:1
2
Lalle Mũ Mun saukar da Littãfi zuwa gare ka, da gaskiya. Sabõda haka, ka bauta wa Allah kanã mai tsarkake addini a gare Shi.
M.Gumi 39:2
3
To, addini tsarkakakke na Allah ne, kuma waɗanda suka riƙi waɗansu majibinta, bã Shi ba, (sunã cẽwa) "Ba mu bauta musu ba fãce dõmin su kusantar da mu zuwa ga Allah, kusantar daraja." Lalle Allah nã yin hukunci a tsakãninsu ga abin da suka zama sunã sãɓãwa a cikinsa. Lalle Allah ba Ya shiryar da wanda yake mai ƙarya, mai kãfirci.
M.Gumi 39:3
4
Dã Allah Yã yi nufin Ya riƙi ɗã, to, lalle sai Ya zãɓa daga abin da Yake halittãwa abin da Yake so. Tsarki ya tabbata a gare Shi. Shĩ ne Allah, Makaɗaici, Mai tĩlastãwa.
M.Gumi 39:4
5
Ya halitta sammai da ƙasã da gaskiya. Yanã shigar da dare a kan rãna, kuma Yanã shigar da rãnã a kan dare kuma Yã hõre rãnã da watã, kõwannensu yanã gudãna zuwa ga ajali ambatacce. To, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai gãfara.
M.Gumi 39:5
6
Yã halitta ku daga rai guda, sa'an nan Ya sanya ma'auranta daga gare shi. Kuma ya saukar muku daga dabbõbin gida nau'i takwas Yanã halitta ku a cikin cikunnan uwayenku, halitta a bãyan wata halitta, a cikin duffai uku. Wannan shĩ ne Allah Ubangijinku. Mulki a gare shi yake. Bãbu abin bautãwa fãce Shi. To, yãya ake karkatar da ku?
M.Gumi 39:6
7
Idan kun kãfirta to, lalle Allah Wadãtacce ne daga barinku, kuma bã Shi yarda da kãfirci ga bãyinSa, kuma idan kun gõde, Zai yarda da ita (gõdiyar) a gare ku, kuma wani rai mai ɗaukar nauyi, bã ya ɗaukar nauyin wani. Sa'an nan kuma makõmarku zuwa ga Ubangijinku take, dõmin Ya bã ku lãbãri game da abin da kuka kasance kunã aikatãwa. Lalle Shĩ, Masani ne ga abin da yake a ainihin zukata.
M.Gumi 39:7
8
Kuma idan wata cũta ta shãfi mutum, sai ya kira Ubangijinsa, yanã mai mai da al'amari zuwa gare Shi, sa'an nan idan Ya jũyar da cũtar da ni'ima ta daga gare Shi, sai ya manta da abin da ya kasance yanã kira zuwa gare shi a gabãnin haka, kuma ya sanya wa Allah waɗansu abõkan tarẽwa dõmin ya ɓatar (da su) daga hanyarSa. Ka ce (masa), "Ka ji dãɗi da kãfircinka, a ɗan lõkaci, lalle kai daga 'yan wutã ne."
M.Gumi 39:8
9
Shin, wanda yake mai tawãli'u sã'õ'in dare, yanã mai sujada kuma yanã mai tsayi ga salla, yanã tsõron Lãhira, kuma yanã fãtan rahamar Ubangijinsa, (yanã daidai da waninsa?) Ka ce: "Ashe, waɗanda suka sani, sunã daidaita da waɗanda ba su sani ba?" Mãsu hankali kawai ke yin tunãni.
M.Gumi 39:9
10
Ka ce: (Allah Ya ce): "Yã bãyĩNa waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Ubangijinku da taƙawa. Waɗanda suka kyautata a cikin wannan dũniya sunã da sakamako mai kyau, kuma ƙasar Allah mai fãɗi ce. Mãsu haƙuri kawai ake cika wa ijãrarsu, bã da wani lissãfi ba.
M.Gumi 39:10
11
Ka ce: "Lalle nĩ, an umurce ni da in bauta wa Allah, inã tsarkake addini a gare Shi.
M.Gumi 39:11
12
Kuma an umurce ni da in kasance farkon mãsu miƙa wuya (ga umurnin Allah).
M.Gumi 39:12
13
Ka ce: "Lalle nĩ inã tsõro, idan na sãɓã wa Ubangijĩna, ga azãbar yini mai girma."
M.Gumi 39:13
14
Ka ce: "Allah nake bautã wa, inã mai tsarkake addinĩna a gare Shi.
M.Gumi 39:14
15
To, ku bauta wa abin da kuke so, waninSa. Ka ce: "Lalle mãsu hasãra, sũ ne waɗanda suka yi hasarar rãyukansu da iyãlansu, a Rãnar ¡iyãma. To, waccan fa, ita ce hasãra bayyananna."
M.Gumi 39:15
16
Sunã da waɗansu inuwõwi na wutã daga samansu, kuma daga ƙasansu akwai waɗansu inuwõwi. Wancan Shĩ ne Allah ke tsõratar da bãyinSa da shi. Yã bãyĩNa! To, ku bĩ Ni da taƙawa.
M.Gumi 39:16
17
Kuma waɗanda suka nĩsanci Shaiɗannu ga bauta musu, kuma suka mai da al'amari ga Allah, sunã da bushãra. To, ka bãyar da bushãra ga bãyiNa.
M.Gumi 39:17
18
Waɗanda ke sauraren magana, sa'an nan su bi mafi kyaunta. waɗancan sũ ne Allah Ya shiryar da su, kuma waɗancan su ne mãsu hankali,
M.Gumi 39:18
19
Shin fa, wanda kalmar azãba ta wajaba a kansa? Shin fa, kanã iya tsãmar da wanda ke a cikin wutã?
M.Gumi 39:19
20
Amma waɗanda suka bi Ubangijinsu da taƙawa, sunã da bẽnãye, daga samansu akwai waɗansu bẽnãye ginannu, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashinsu. Alkawarin Allah. Allah bã Ya sãɓã wa alkawarinSa.
M.Gumi 39:20
21
Shin, ba ka gani ba cẽwa lalle Allah Yã saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Yã gudãnar da shi yanã marẽmari a cikin ƙasã sa'an nan Yã fitar da shũka game da shi, launukan shũkar mãsu sãɓãnin jũna sa'annan shũkar ta ƙeƙashe har ka gan ta fatsifatsi, sa'an nan Allah Ya sanya ta dandaƙaƙƙiya? Lalle ne ga wancan akwai tunãtarwa ga mãsu hankali (ga iyãwar gudãnar da ruwa a cikin gidãjen Aljanna).
M.Gumi 39:21
22
Shin fa, wanda Allah Ya buɗa ƙirjinsa, dõmin Musulunci sa'an nan shi yanã a kan haske daga Ubangijinsa, (zai zama kamar waninsa)? To, bone yã tabbata ga maƙeƙasa zukãtansu daga ambaton Allah. Waɗancan sunã a cikin wata ɓata bayyananna.
M.Gumi 39:22
23
Allah Ya sassaukar da mafi kyaun lãbãri, Littãfi mai kama da jũna, wanda ake konkoma karãtunsa fãtun waɗanda ke tsõron Ubangijinsu, sunã tãƙura sabõda Shi, sa'an nan fãtunsu da zukãtansu su yi laushi zuwa ga ambaton Allah. Waccan ita ce shiryarwar Allah, Yanã shiryar da wanda Ya so game da ita. Kuma wanda Allah Ya ɓatar, to, bã shi da wani mai shiryarwa.
M.Gumi 39:23
24
Shin fa, wanda ke kãre mũguwar azãba da fuskarsa (yanã zama kamar waninsa) a Rãnar ƙiyãma? Kuma a ce wa azzãlumai, "Ku ɗanɗani abin da kuka kasance kunã aikatãwa."
M.Gumi 39:24
25
Waɗanda ke a gabãninsu, sun ƙaryata, sai azãba ta jẽ musu daga inda ba su sani ba.
M.Gumi 39:25
26
Sai Allah Ya ɗanɗana musu azãbar wulãkanci a cikin rãyuwar dũniya, kuma lalle azãbar Lãhira ita ce mafi girma, dã sun kasance sunã da sani.
M.Gumi 39:26
27
Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun buga wa mutãne a, cikin wannan Alƙur'ãni, daga kõwane misãli, ɗammãninsu su yi tunãni.
M.Gumi 39:27
28
Abin karantãwa ne na Lãrabci, ba mai wata karkata ba, ɗammãninsu, su yi taƙawa.
M.Gumi 39:28
29
Allah Yã buga misãli; wani mutum (bãwa) a cikinsa akwai mãsu tarayya, mãsu mũgun hãlin jãyayya, da wani mutum (bãwa) dukansa ga wani mutum. Shin, zã su daidaita ga misãli? Gõdiya ta tabbata ga Allah (a kan bayãni). Ã'a, mafi yawan mutãne ba su sani ba.
M.Gumi 39:29
30
Lalle kai mai mutuwa ne, kuma su mã lalle mãsu mutuwa ne.
M.Gumi 39:30