Ana SayfaMealler › M.Gumi
MG

M.Gumi

M.Gumi
M.Gumi meali ile okumaya başla
Yasin 1 / 83
1
Y. S̃.
M.Gumi 36:1
2
Inã rantsuwa da Al-ƙur'ãni Mai hikima.
M.Gumi 36:2
3
Lalle kai, haƙĩƙa kanã cikinManzanni.
M.Gumi 36:3
4
A kan hanya madaidaiciya.
M.Gumi 36:4
5
(Allah Ya saukar da Al-kur'ãni) saukarwar Mabuwãyi, Mai jin ƙai.
M.Gumi 36:5
6
Dõmin ka yi gargaɗi ga waɗansu mutãne da ba a yi gargaɗi ga ubanninsu ba, sabõda haka sũmasu rafkana ne.
M.Gumi 36:6
7
Lalle, haƙĩƙa, kalma tã wajaba a kan mafi yawansu, dõmin sũ, bã zã su yi ĩmãni ba.
M.Gumi 36:7
8
Lalle Mũ, Mun sanya ƙuƙumma a cikin wuyõyinsu, sa'an nan sũ (ƙuƙumman sun kai) har zuwa ga haɓõɓinsu, sabõda haka, sũ banƙararru ne.
M.Gumi 36:8
9
Kuma Muka sanya wata tõshiya a gaba gare su, da wata tõshiya a bãyansu, sabõda haka Muka rufe su, sai suka zama bã su gani.
M.Gumi 36:9
10
Kuma daidai yake a gare su, shin, ka yi musu gargaɗi kõ ba ka yi musu gargaɗi ba, sũ bã zã su yi ĩmãni ba.
M.Gumi 36:10
11
Kanã yin gargaɗi kawai ga wanda ya bi Alƙur'ãni ne, kuma ya ji tsõron mai rahama a fake. To, ka yi masa bushãra da gãfara da wani sakamako na karimci.
M.Gumi 36:11
12
Lalle Mũ, Mũ ne ke rãyar da matattu kuma Mu rubũta abin da suka gabãtar, da gurãbunsu, kuma kõwane abu Mun ƙididdige shi, a cikin babban Littãfi Mabayyani.
M.Gumi 36:12
13
Kuma ka buga musu misãli: Waɗansu ma'abũta alƙarya, a lõkacin da Manzanni suka jẽ mata.
M.Gumi 36:13
14
A lõkacin da Muka aika (Manzannin) biyu zuwa gare su, sai suka ƙaryata su, sa'an nan Muka ƙarfafa (su) da na uku, sai suka ce: "Lalle mũ, Manzanni ne zuwa gare ku."
M.Gumi 36:14
15
Suka ce: "Kũ ba ku zamo bafãce mutãne ne kamarmu kuma Mai rahama bai saukar da kõme ba, ba ku zamo ba fãce ƙarya kuke yi."
M.Gumi 36:15
16
Suka ce: "Ubangijinmu Yã sani, lalle mũ, haƙiƙa Manzanni nezuwa gare ku."
M.Gumi 36:16
17
Kuma bãbu abin da ke kanmu, fãce iyar da manzanci bayyananne.
M.Gumi 36:17
18
Suka ce: "Lalle mũ munã shu'umci da ku! Haƙĩƙa idan ba ku, hanu ba, haƙĩƙa, zã mu jẽfe ku, kuma haƙĩƙa wata azãba mai raɗaɗi daga gare mu zã ta shãfe ku."
M.Gumi 36:18
19
Suka ce: "Shu'umcinku, yanã tãre da ku. Ashe, dõmin an tunãtar da ku? Ã'a, kũ dai mutãne ne mãsu ƙẽtare haddi."
M.Gumi 36:19
20
Kuma wani mutum daga mafi nĩsan birnin ya je, yanã tafiya da gaggãwa, ya ce: "Ya mutãnẽna! Ku bi Manzannin nan.
M.Gumi 36:20
21
Ku bi waɗanda bã su tambayar ku wata ijãra kuma sũ shiryayyu ne.
M.Gumi 36:21
22
Kuma mene ne a gare ni, bã zan bauta wa Wanda Ya ƙãga halittata ba, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku?
M.Gumi 36:22
23
Shin, zan riƙi waninSa abũbuwan bautãwa? Idan Mai rahama Ya nufe ni da wata cũta, to cẽtonsu bã ya amfanĩna da kõme, kuma bã za su iya tsãmar da ni bã.
M.Gumi 36:23
24
Lalle nĩ, a lõkacin nan, tabbas, inã a cikin ɓata bayyananna.
M.Gumi 36:24
25
Lalle ni, nã yi ĩmãni da Ubangijinku, sabõda haka ku saurãre ni.
M.Gumi 36:25
26
Aka ce (masa), "Ka shiga Aljanna." Ya ce, "Dã dai a ce mutãnẽna sunã iya sani."
M.Gumi 36:26
27
Game da gãfarar da Ubangijjĩna ya yi mini, kuma Ya sanya ni a cikin waɗanda aka girmama.
M.Gumi 36:27
28
Kuma ba Mu saukar da waɗansu runduna ba daga sama a kan (halaka) mutãnensa, daga bãyansa, kuma bã zã Mu kasance. Mãsu saukarwa ba.
M.Gumi 36:28
29
Ba ta kasance ba face tsawa guda, sa'an nan sai gã su sõmammu.
M.Gumi 36:29
30
Yã nadãma a kan bãyĩNa! Wani Manzo bã ya zuwa gare su fãce sun kasance sunã mãsu yi masa izgili.
M.Gumi 36:30