Ana SayfaMealler › M.Gumi
MG

M.Gumi

M.Gumi
M.Gumi meali ile okumaya başla
Ankebut 1 / 69
1
A. L̃. M̃.
M.Gumi 29:1
2
Ashe, mutãne sun yi zaton a bar su su ce: "Mun yi ĩmãni," alhãli kuwa bã zã a fitine su ba?"
M.Gumi 29:2
3
Kuma lalle Mun fitini waɗanda ke a gabãninsu, dõmin lalle Allah Ya san waɗanda suka yi gaskiya, kuma lalle Ya san maƙaryata.
M.Gumi 29:3
4
Kõ waɗanda ke aikata miyãgun ayyuka sun yi zaton su tsẽre Mana? Abin da suke hukuntãwa ya mũnana.
M.Gumi 29:4
5
Wanda ya kasance yanã fãtan gamuwa da Al1ah to lalle ajalin Allah mai zuwa ne, kuma (Allah) Shĩ ne Mai ji, Masani.
M.Gumi 29:5
6
Kuma wanda ya yi jihãdi, to, yanã yin jihãdin ne dõmin kansa. lalle Allah haƙĩƙa waɗatacce ne daga barin tãlikai.
M.Gumi 29:6
7
Kuma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, lalle Munã kankare musu miyãgun ayyukansu, kuma lalle Munã sãka musu da mafi kyaun abin da suka kasance sunã aikatãwa.
M.Gumi 29:7
8
Kuma Mun yi wa mutum wasiyyar kyautatãwa ga uwayensa, kuma idan sun tsananta maka dõmin ka yi shirki da Ni game da abin da bã ka da ilmi gare shi, to, kada ka yi musu ɗã'ã. Zuwa gare Ni makõmarku take sa'an nan In bã ku lãbari ga abin da kuka kasance kunã aikatãwa.
M.Gumi 29:8
9
Kuma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, lalle Munã shigar da su a cikin mutãnen kirki.
M.Gumi 29:9
10
Kuma daga cikin mutãne akwai mai cẽwa, 'Mun yi ĩmãni da Allah" sa'an nan idan aka cũce shi wajen aikin Allah, sai ya sanya fitinar mutãne kamar azãbar Allah kuma lalle idan taimakon Ubangijinka ya zo, haƙĩƙa, ya kan ce: "Lalle mũ mun kasance tãre da ku." shin, Allah bai zama Mafi sani ba ga abin da ke a cikin ƙirãzan halittunSa?
M.Gumi 29:10
11
Kuma lalle Allah na sanin waɗanda suka yi ĩmãni kuma lalle Yanã sanin munfukai.
M.Gumi 29:11
12
Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce wa waɗanda suka yi ĩmãni, "Ku bi hanyarmu, kuma Mu ɗauki laifuffukanku," alhãli kõwa ba su zamo mãsu ɗauka da a kõme ba daga laifuffukansu. Lalle sũ maƙaryata ne.
M.Gumi 29:12
13
Kuma lalle sunã ɗaukar kãyan nauyinsu da waɗansu nauyãyan kãya tãre da kãyan nauyinsu, kuma lalle zã a tambaye su a Rãnar ¡iyama game da abin da suka kasance sunã ƙirƙirãwa na ƙarya.
M.Gumi 29:13
14
Kuma lalle Mun aika Nũhu zuwa ga mutãnensa, sai ya zauna a cikinsu shẽkara dubu fãce shẽkara hamsin, sa'an nan cikowar (¦ũfãna) ta kãmã su, alhãli kuwa sũ ne mãsu zãlunci.
M.Gumi 29:14
15
Sa'an nan Muka tsĩrar da shi da mutãnen jirgin, kuma Muka sanya jirgin ya zama wata ãyã ga tãlikai.
M.Gumi 29:15
16
Da Ibrãhĩm a lõkacin da ya ce wa mutãnensa, "Ku bautã wa Allah ku bĩ Shi da taƙawa. Wannan Shĩ ne alhẽri a gare ku idan kun kasance kunã sani.
M.Gumi 29:16
17
Abin da dai kuke bautãwa, baiein Allah, gumaka ne, kuma kun ƙirƙira ƙarya. Lalle waɗannan da kuke bauta wa baicin Allah, bã su mallakã muku arziki. Sabõda haka ku nẽmi arziki a wurin Allah kawai, kuma ku bauta Masa, kuma ku yi gõdiya zuwa gare Shi. Zuwa gare Shi ake mayar da ku.
M.Gumi 29:17
18
Kuma idan kun ƙaryata, to, lalle waɗansu al'ummõmi a gabãninku sun ƙaryata, kuma bãbu abin da ke kan Manzo, fãce iyar da manzanci, iyarwa bayyananna.
M.Gumi 29:18
19
Shin, ba su ga yadda Allah ke fãra yin halitta ba, sa'an nan kuma Ya mayar da ita? Lalle wannan abu ne mai sauƙi ga Allah.
M.Gumi 29:19
20
Ka ce: "Ku yi tafiya cikin ƙasa, sa'an nan ku dũba yadda (Allah) Ya fãra yin halitta, sa'an nan kuma Allah Yanã ƙãga wata halittar mayarwa. Lalle Allah Mai ikon yi ne a kan kõme.
M.Gumi 29:20
21
Yanã azabta wanda Ya so, kuma Yanã jin ƙan wanda Ya so. Kuma zuwa gare shi ake jũyaku.
M.Gumi 29:21
22
Kuma ba ku zamo mãsu buwãya ba a cikin ƙasã, kuma haka a cikin sama kuma bã ku da wani majiɓinci wanda ba Allah ba, kuma ha ku da wani mataimaki.
M.Gumi 29:22
23
Kuma waɗanda suka kãfirta da ãyõyin Allah da gamuwa da shi, waɗannan sun yanke ƙauna daga rahamaTa kuma waɗannan sunã da wata azãba mai raɗaɗi.
M.Gumi 29:23
24
Sa'an nan bãbu abin da ya kasance jawãbin mutãnensa (Ibrãhĩm) fãce dai suka ce: "Ku kashe shi kõ, ku ƙõnã shi," Sai Allah Ya tsĩrar da shi daga wutã. Lallea cikin wannan akwai ayõyi ga mutãnen da ke yin ĩmãni.
M.Gumi 29:24
25
Kuma Ibrahĩm ya ce "Bãbu abin da kuka yi sai dai kub bar Allah kun riƙi gumãka sabõda sõyayyar tsakãninku a cikin rãyuwar dũniya, a'an nan a Rãnar ¡iyãma sãshinku zai kãfirce wa sãshi, kuma makõmarku ita ce wutã kuma bã ku da waɗansu mataimaka."
M.Gumi 29:25
26
Sai Lũɗu ya yi ĩmãni da shi. Kuma Ibrãhĩm ya ce: "Lallenĩ mai ƙaura ne zuwa ga Ubangijina. Lalle Shĩ Shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima."
M.Gumi 29:26
27
Kuma Muka bã shi Ishãƙa da Ya'aƙũba, kuma Muka sanya Annabci da littãfi a cikin zuriyarsa. Kuma Mun bã shi sakamakonsa a dũniya, kuma lalle shĩ a Lãhira, tabbas, yanã a cikin sãlihai.
M.Gumi 29:27
28
Da Lũɗu, a lõkacin daya ce wa mutãnensa, "Lalle kũ, haƙĩƙa kunã jẽ wa alfãsha wadda wani mahalũƙi daga cikin dũniya bai riga ku gare ta ba.
M.Gumi 29:28
29
Ashe, lalle kũ kunã je wa maza, kuma ku yi fashin hanya kuma ku je, a cikin majalisarku da abin da bã shi da kyau? To, jawãbin mutãnensa bai kasance ba fãce dai sun ce: 'Ka zo mana da azãbar Allah, idan ka kasance daga mãsu gaskiya.'
M.Gumi 29:29
30
Ya ce: "Ya Ubangijĩna! Ka taimake ni a kan mutãnen nan maɓarnata."
M.Gumi 29:30