Ana SayfaMealler › M.Gumi
MG

M.Gumi

M.Gumi
M.Gumi meali ile okumaya başla
Neml 1 / 93
1
¦. S̃. Waɗancan ãyõyinAlƙur'ãni ne da Littãfi mai bayyanawa.
M.Gumi 27:1
2
Shiriya ce da bushãra ga mũminai.
M.Gumi 27:2
3
Waɗanda suke tsayar da salla kuma su bãyar da zakka, alhãli kuwa sũ, game da Lãhira, to, sũ, sunã yin yaƙĩni.
M.Gumi 27:3
4
Lalle ne waɗanda suke bã su yin ĩmãni da Lãhira, Mun ƙawãta musu ayyukansu, sabõda haka sunã ɗimuwa.
M.Gumi 27:4
5
Waɗannan ne waɗanda suke sunã da mugunyar azãba (a dũniya), kuma sũ, a Lãhira, sũ ne mafiya hasãra.
M.Gumi 27:5
6
Kuma lalle ne haƙĩƙa, anã haɗa ka da Alƙur'ãni daga gun Mai hikima, Masani.
M.Gumi 27:6
7
A lõkacin da Mũsã ya ce wa iyãlinsa "Lalle ni, na tsinkãyi wata wuta, ni mai zo muku daga gare ta ne, da wani lãbari, ko kuwa mai zo muku ne da Yũla, makãmashi, tsammãninku, ku ji ɗimi."
M.Gumi 27:7
8
To, a lõkacin da ya jẽ mata, sai aka kira shi cẽwa, "An tsarkake wanda yake cikin (wurin) wutar da yanda yake a gẽfenta kuma tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin halittu."
M.Gumi 27:8
9
Yã Mũsã lalle ne shi, Nĩ ne Allah, Mabuwãyi, Mai hikima.
M.Gumi 27:9
10
Kuma ka jẽfa sandarka. To, a lõkacin da ya gan ta tanã girgiza kamar dai ita ƙaramin macĩji ne, sai ya jũya yanã mai bãyar da bãya, kuma bai kõma ba, "Yã Musã! Kada ka ji tsõro lalle Ni, Manzanni bã sujin tsõro a wuriNa."
M.Gumi 27:10
11
Sai wanda ya yi zãlunci, sa'an nan ya musanya kyau a bãyan cũta, to, lalle Nĩ, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
M.Gumi 27:11
12
Kuma ka shigar da hannunka a cikin wuyan rĩgarka, ya fita fari, bãbu wata cũta, a cikinwasu ãyõyi tara zuwa ga Fir'auna da mutãnensa. Lalle ne sũ, sun kasance mutãne ne fãsiƙai.
M.Gumi 27:12
13
To, a lõkacin da ãyõyinMu suka jẽ musu, sunã mãsu wãyar da kai suka ce wannan sihiri ne bayyananne.
M.Gumi 27:13
14
Kuma suka yi musunsu, alhãli zukãtansu sun natsu da su dõmin zãlunci da girman kai. To, ka dũbi yadda ãƙibar maɓarnata ta kasance.
M.Gumi 27:14
15
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bai wa Dãwũda da Sulaimãn ilmi kuma suka ce: "Gõdiya ta tabbata ga Allah, Wanda Ya fĩfĩta mu a kan mãsu yawa daga bãyinSa mũminai."
M.Gumi 27:15
16
Kuma sulaimãn ya gãji Dãwũda ya ce: "Yã ku mutãne! An sanar da mu maganar tsuntsãye, kuma an bã mu daga kõwane abu. Lalle ne wannan haƙĩƙa shi ne falalar (Allah) bayyananna."
M.Gumi 27:16
17
Kuma aka tattara, dõmin Sulaimãn, rundunõninsa, daga aljannu da mutãne da tsuntsãye, to, sũ anã kange su (ga tafiya).
M.Gumi 27:17
18
Har a lõkacin da suka je a kan rãfin turũruwa wata turũruwa ta ce, "Yã kũ jama'ar turũruwa! Ku shiga gidãjenku, kada Sulaimãn da rundunõninsa su kakkarya ku, alhãli kuwa sũ, ba su sani ba."
M.Gumi 27:18
19
Sai ya yi murmushi yanã mai dãriya daga maganarta, kuma ya ce, "Yã Ubangijĩna! Ka cũsa mini in gõde wa ni'imarKa wadda Ka ni'imta ta a gare ni da kuma ga mahaifãna biyu, kuma in aikata aiki na ƙwarai, wanda Kake yarda da shi, kuma Ka shigar da ni, sabõda rahamarKa, a cikin bãyinKa sãlihai."
M.Gumi 27:19
20
Kuma ya binciki tsuntsãye, sai ya ce: "Me ya kãre ni bã ni ganin hudhudu, kõ ya kasance daga mãsu fakuwa ne?"
M.Gumi 27:20
21
Lalle ne zã ni azabta shi azãba mai tsanani kõ kuwa lalle in yanka shi, kõ kuwa lalle ya zo mini da dalĩli bayyananne.
M.Gumi 27:21
22
Sai ya zauna bã nẽsa ba, sa'an nan ya ce: "Nã san abin da ba ka sani ba, kuma na zo maka daga Saba da wani lãbari tabbatacce."
M.Gumi 27:22
23
Lalle ni nã sãmi wata mace wadda tanã mulkinsu kuma an bã ta daga dukkan kõme, kuma tanã da gadon sarauta mai girma.
M.Gumi 27:23
24
Na sãme ta ita da mutãnenta, sunã yin sujada ga rãnã, baicin Allah, kuma Shaiɗan ya ƙawãce musu ayyukansu, sabõda haka ya karkatar da su daga hanya, sa'an nan sũ, ba su shiryuwa.
M.Gumi 27:24
25
Ga su yi sujada ga Allah Wanda Yake fitar da abin da yake a ɓõye, a cikin sammai da ƙasa, kuma Yã san abin da kuke ɓõyẽwada abin da kuke bayyanãwa.
M.Gumi 27:25
26
Allah bãbu abin bautãwa fãce shĩ Ubangijin Al'arshi, mai girma.
M.Gumi 27:26
27
Ya ce: "Za mu dũba shin kã yi gaskiya ne, kõ kuwa kã kasance daga maƙaryata?"
M.Gumi 27:27
28
Ka tafi da takardata wannan, sa'an nan ka jẽfa ta zuwa gare su, sa'an nan kuma ka jũya daga barinsu, sa'an nan ka ga mẽne ne suke mayarwa.
M.Gumi 27:28
29
Ta ce: "Yã kũ mashawarta! Lalle ne, an jẽfo, zuwa gareni, wata takarda mai girma."
M.Gumi 27:29
30
Lalle ita daga Sulaiman take, kuma lalle ita da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai ne.
M.Gumi 27:30