2
Waɗancan ãyõyin Littãfi ne bayyananne.
3
Tsammãninka kai mai halakar da ranka ne, dõmin ba su kasance mũminai ba!
4
Idan Mun so zã Mu saukar, a kansu, da wata ãyã daga sama, sai wuyõyinsu su yini sabõda ita sunã mãsu ƙasƙantar da kai.
5
Kuma wata tunãtarwa ba ta jẽ musu ba, daga Mai rahama, sãbuwa, fãce sun kasance daga barinta sunã mãsu bijirẽwa.
6
To, lalle ne, sun ƙaryata, to, lãbãran abin da suka kasance sunã yi na izgili da shi zã ya je musu.
7
Shin, ba su dũba ba zuwa ga ƙasa, da yawa Muka tsirar a cikinta, daga dukan nau'i mai kyau?
8
Lalle ne, a cikin wancan akwai ãyã, kuma mafi yawansu ba su kasance mũminai ba.
9
Kuma lalle ne, Ubangijinka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai rahama.
10
Kuma a lõkacin da Ubangijinka Ya kirãyi Mũsã, "Ka je wa mutãnen nan azzãlumai.
11
Mutãnen Fir'auna bã zã su yi taƙawa ba?
12
Ya ce: "Ya Ubangijĩna, nĩ inã tsõron su ƙaryata ni.
13
Kuma ƙirjĩna ya yi ƙunci kuma harshẽna bã zai saku ba sabõda haka ka aika zuwa ga Harũna.
14
Kuma sunã da wani laifi a kaina, sabõda haka inã tsõron kada su kashe ni.
15
Ya ce: "Kayya! Ku tafi, kũ biyu, da ÃyõyinMu. Lalle ne, Munã tãre da ku Munã Mãsu saurãre."
16
Sai ku je wa Fir'auna, sa'an nan ku ce, Lalle ne, mu, Manzannin Ubangijin halitta ne.
17
Ka saki Banĩ Isrã'ila tãre da mu.
18
Ya ce: "Shin, ba mu yi rẽnonka ba a cikinmu kanã jãrĩri, kuma ka zauna a cikinmu shẽkarudaga lõkacin rãyuwarka?"
19
Kuma ka aikata aikinka wanda ka aikata alhãli kai kanã daga butulai?
20
Ya ce: "Na aikata shi a lõkacin inã daga mãsu jãhilcin hushi."
21
Sabõda haka na gudu daga gãre ku a lõkacin da na ji tsõronku, sai Ubangijĩna Ya bã ni hukunci, kuma Ya sanya ni daga Manzanni.
22
Kuma waccan ni'ima ce, kanã gõrint a kaina, dõmin kã bautar da Banĩ Isrã'ĩla.
23
Fir'auna ya ce: "Kuma mene ne Ubangijin halittu?"
24
Ya ce: "Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, idan kun kasance mãsu ƙarfin ĩmãni."
25
Ya ce wa waɗanda suke a gẽfensa, "Bã za ku saurãra ba?"
26
Ya ce: "Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku na farko."
27
Ya ce: "Lalle ne Manzonku, wanda aka aiko zuwa gare ku, haƙi ƙa, mahaukaci ne."
28
Ya ce: "Ubangijin mafitar rãnã da maɓũyarta da abin dayake a tsakaninsu, idan kun kasance kunã hankalta."
29
Ya ce: "Lalle ne idan ka riƙi wani abin bautãwa wanĩna haƙĩƙa, inã sanyã ka daga ɗaurarru."
30
Ya ce: "Ashe, kuma kõ dã nã zõ maka da wani, abu mai bayyanãwa?"
Sonraki 30 ayet →