Ana SayfaMealler › M.Gumi
MG

M.Gumi

M.Gumi
M.Gumi meali ile okumaya başla
Ta Ha 1 / 135
1
¦.H.
M.Gumi 20:1
2
Ba Mu saukar da Alƙur'ãni a gare ka dõmin ka wahala ba.
M.Gumi 20:2
3
Fãce dõmin tunãtarwa ga wanda ke tsõron Allah.
M.Gumi 20:3
4
(An saukar da shi) saukarwa daga wanda Ya halitta ƙasa da sammai maɗaukaka.
M.Gumi 20:4
5
Mai rahama, Ya daidaita a kan Al'arshi.
M.Gumi 20:5
6
Abin da yake a cikin sammai nãSa ne, da abin da yake a cikin ƙasa da abin da yake a tsakãninsu da abin da ke ƙarƙashin turɓãya.
M.Gumi 20:6
7
Kuma idan ka bayyana da magana, to, lalle Shi, Yanã sanin asĩri da mafi bõyuwa.
M.Gumi 20:7
8
Allah bãbu abin bautãwa fãce Shi. Yanã da sunãye mafiya kyau.
M.Gumi 20:8
9
Kuma shin, lãbarin Mũsã yãje maka?
M.Gumi 20:9
10
A lõkacin da ya ga wata wuta, sai ya ce wa iyãlinsa, "Ku dãkata. Lalle ne nĩ, na tsinkãyi wata wuta tsammãnĩna in zo mukuda makãmashi daga gare ta, kõ kuwa in sãmi wata shiriya a kan wutar."
M.Gumi 20:10
11
Sa'an nan a lõkacin da ya je mata, aka kira shi, "Ya Mũsã!"
M.Gumi 20:11
12
Lalle ne, Nĩ ne Ubangijnka, sai ka ɗẽbe takalmanka Lalle ne kanã a rãfin nan abin tsarkakẽwa, ¦uwa.
M.Gumi 20:12
13
Kuma Nĩ Nã zãɓe ka. Sai ka saurãra ga abin da ake yin wahayi.
M.Gumi 20:13
14
Lalle, Nĩ Ni ne Allah. Bãbu abin bautawa fãce Ni. Sai ka bauta Mini, kuma ka tsayar da salla dõmin tuna Ni.
M.Gumi 20:14
15
Lalle ne Sa'a mai zuwa ce, lnã kusa da In ɓõye ta dõmin a sãka wa dukan rai da abin da yake aikatãwa.
M.Gumi 20:15
16
Sabõda haka, kada wanda bã ya yin ĩmãni da ita kumaya bi son zuciyarsa, ya taushe ka daga gare ta har ka halaka.
M.Gumi 20:16
17
Kuma wãce ce waccan ga dãmanka yã Mũsa!
M.Gumi 20:17
18
Ya ce: "Ita sandãta ce, inã dõgara a kanta, kuma inã kakkaɓar ganye da ita a kan ƙananan bisãshẽna kuma inã da waɗansu bukãtõci na dabam a gare ta."
M.Gumi 20:18
19
Ya ce: "Ka yi jĩfa da ĩta, yã Mũsã!"
M.Gumi 20:19
20
Sai ya jẽfa ta. Sai gã ta dabbar macĩjiya, tanã tafiya da gaggãwa.
M.Gumi 20:20
21
Ya ce: "Ka kãma ta kuma kada ka ji tsõro. Za Mu mayar da ita ga hãlinta na farko."
M.Gumi 20:21
22
Kuma ka haɗa hannunka zuwa ga damtsenka, ya fita yanã fari, bãbu sõfane, wata ãyã ta dabam.
M.Gumi 20:22
23
Dõmin Mu nũna maka daga ãyõyinMu manya.
M.Gumi 20:23
24
Ka tafi zuwa ga Fĩr'auna. Lalle shĩ ya ƙẽtare haddi (da girman kai).
M.Gumi 20:24
25
Ya ce: "Ya Ubangiji! Ka buɗa mini, ƙirjĩna.
M.Gumi 20:25
26
Kuma ka sauƙaƙe mini al'amarĩna.
M.Gumi 20:26
27
Kuma Ka warware mini wani ƙulli daga harshẽna.
M.Gumi 20:27
28
Su fahimci maganãta.
M.Gumi 20:28
29
Kuma Ka sanya mini wani mataimaki daga mutãnena.
M.Gumi 20:29
30
Hãrũna ɗan'uwana.
M.Gumi 20:30