Ana SayfaMealler › M.Gumi
MG

M.Gumi

M.Gumi
M.Gumi meali ile okumaya başla
Meryem 1 / 98
1
K̃.H. Y.I. Ṣ̃.
M.Gumi 19:1
2
Ambaton rahamar Ubangijinka ne ga BawanSa Zakariyya.
M.Gumi 19:2
3
A lõkacin da ya kirãyi Ubangijinsa, kira ɓõyayye.
M.Gumi 19:3
4
Ya ce: "Yã Ubangijina! Lalle ne nĩ, ƙashi na daga gare ni ya yi rauni, kuma kaina ya kunnu da furfura, kuma ban kasance marashin arziki ba game da kiranKa, yã Ubangiji!"
M.Gumi 19:4
5
Kuma lalle nĩ, na ji tsõron dangi a bãyãna, kuma mãtãta ta kasance bakarãriya! Sai ka bã ni wani mataimaki daga wajenKa.
M.Gumi 19:5
6
Ya gãjẽ ni, kuma ya yi gãdo daga gidan Yãƙũba. Kuma Ka sanya shi yardajje, yã Ubangiji!
M.Gumi 19:6
7
(Allah Ya karɓa) "Yã zakariyya! Lalle ne Mũ, Munã yi maka bushãra da wani yãro, sunansa Yahaya. Ba Mu sanya masa wani takwara ba a gabãni."
M.Gumi 19:7
8
Ya ce: "Yã Ubangijĩna! Yãya wani yãro zai kasance a gare ni, alhãli kuwa mãtãta ta kasance bakarãriya, kuma gã shi nã kai ga matuƙa ta tsũfa?"
M.Gumi 19:8
9
Ya ce: "Kamar wancan Ubangijinka Ya ce. Shĩ, a gare Ni mai sauƙi ne, kuma haƙĩƙa Na halitta ka a gabãnin haka, alhãli ba ka kasance kõme ba."
M.Gumi 19:9
10
Ya ce: "Yã Ubangijina! Ka sanya mini alãma." Ya ce: "Alamarka ita ce ka kãsa yi wa mutãne magana a darũruwa uku daidai."
M.Gumi 19:10
11
Sai ya fita a kan mutãnensa daga masallãci, sa'an nan ya yi ishãra zuwa gare su da cẽwa, "Ku yi tasbĩhi sãfe da yamma."
M.Gumi 19:11
12
Yã Yahaya! Ka kãma littãfi da ƙarfi. Kuma Muka bã shi hukunci yanã yãro.
M.Gumi 19:12
13
Kuma (Muka sanya shi) abin girmamãwa daga gunMu, kuma mai albarka, kuma ya kasance mai ɗã'ã da taƙawa.
M.Gumi 19:13
14
Kuma mai biyayya ga mahaifansa biyu, kuma bai kasance mai girman kai mai sãɓo ba.
M.Gumi 19:14
15
Kuma aminci ya tabbata a gare shi a rãnar da aka haife shi da rãnar da yake mutuwa da rãnar da ake tãyar da shi yanã mai rai.
M.Gumi 19:15
16
Kuma ka ambaci Maryamu a cikin Littãfi, a lõkacin da ta tsallake daga mutãnenta a wani wuri, a gẽfen gabas.
M.Gumi 19:16
17
Sa'an nan ta riƙi wani shãmaki daga barinsu. Sai Muka aika rũhinMu zuwa gare ta. Sai ya bayyana a gare ta da siffar mutum madaidaci.
M.Gumi 19:17
18
Ta ce: "Lalle nĩ inã nẽman tsari ga Mai, rahama daga gare ka, idan ka kasance mai tsaron addini!"
M.Gumi 19:18
19
Ya ce: "Abin sani kawai, ni Manzon Ubangijinki ne dõmin in bãyar da wani yãro tsarkakke gare ki."
M.Gumi 19:19
20
Ta ce: "A inã yãro zai kasance a gare ni alhãli kuwa wani mutum bai shãfe ni ba, kuma ban kasance kãruwa ba?"
M.Gumi 19:20
21
Ya ce: "Kamar wancan Ubangijinki Ya ce. Shĩ, a gare Ni mai sauƙi ne. Kuma dõmin Mu sanya shi wata alãma ga mutãne, kuma wata rahama ce daga gare Mu.' Kuma abin yã kasance wani al'amari hukuntacce."
M.Gumi 19:21
22
Sai ta yi cikinsa, sai ta tsallake da shi ga wani wuri mai nĩsa.
M.Gumi 19:22
23
Sai nãƙuda ta kai ta zuwa ga wani kututturen dabĩniya, ta ce "Kaitona, dã dai na mutu a gabãnin wannan kuma na kasance wani abu wulakantacce wanda aka manta!"
M.Gumi 19:23
24
Sai (yãron da ta haifa) ya kira ta daga ƙarƙashinta, "Kada ki yi baƙin ciki! Haƙĩƙa Ubangijinki Ya sanya wani marmaro a ƙarƙashinki.
M.Gumi 19:24
25
Kuma ki girgiza zuwa gare ki game da kututturen dabĩnon ya zuba a kanki yanã 'ya'yan dabĩno, ruɗabi nunannu.
M.Gumi 19:25
26
Sai ki ci kuma ki sha kuma ki ji sanyi ga idãnunki. To, idan kin ga wani aya daga mutãne, sai ki ce, 'Lalle nĩ, na yi alwãshin azumi dõmin Mai rahama sabõda haka bã zan yi wa wani mutum magana ba.
M.Gumi 19:26
27
Sai ta je wa mutãnenta tanã auke da shi. Suka ce: "Yã Maryamu! Lalle ne, haƙĩƙa kin zo da wani abu mai girma!
M.Gumi 19:27
28
Yã 'yar'uwar Hãrũna! Ubanki bai kasance mutumin alfãsha ba, kuma uwarki ba ta kasance kãruwa ba.
M.Gumi 19:28
29
Sai ta yi ishãra zuwa gare shi, suka ce: "Yãya zã mu yi magana da wanda ya kasance a cikin shimfiar tsumma yanã jãrĩri?"
M.Gumi 19:29
30
Ya ce: "Lalle ne, nĩ bãwan Allah ne Allah Yã bã ni Littãfi kuma Ya sanya ni Annabi."
M.Gumi 19:30