1
A. L̃.R. Waɗancan ãyoyin Littãfi mai bayyanãwa ne.
2
Lalle ne Mũ, Mun saukar da shi, yanã abin karantãwa na Lãrabci; tsammãninkũ, kunã hankalta.
3
Mũ, Munã bãyar da lãbãri a gare ka, mafi kyãwon lãbãri ga abin da Muka yi wahayin wannan Alƙur'ãni zuwa gare ka. Kuma lalle ne kã kasance a gabãninsa, haƙĩƙa, daga gafalallu.
4
A lõkacin da Yũsufu ya ce wa ubansa, "Yã bãba! Lalle ne nĩ, nã ga taurãri gõma shã ɗaya, da rãnã da watã. Na gan su sunã mãsu sujada a gare ni."
5
Ya ce: "Ya ƙaramin ɗãna! Kada ka faɗi mafarkinka ga 'yan'uwanka, har su ƙulla maka wani kaidi. Lalle ne Shaidan ga mutum, haƙĩƙa, maƙiyi ne bayyanãnne.
6
Kuma kãmar wancan ne, Ubangijinka Yake zãɓen ka, kuma Ya sanar da kai daga fassarar lãbãrai, kuma ya cika ni'imõminSa a kanka, kuma a kan gidan Yãƙũba kãmar yadda ya cika su a kan ubanninka biyu, a gabãni, Ibrãhĩm da Is'hãƙa. Lalle Ubangijinka ne Masani, Mai hikima.
7
Lalle ne, haƙĩƙa, ãyõyi sun kasance ga Yũsufu da 'yan'uwansa dõmin mãsu tambaya.
8
A lõkacin da suka ce: lalle ne Yũsufu da ɗan'uwansa ne mafiya sõyuwa ga ubanmu daga gare mu, alhãli kuwa mũ jama'a guda ne. Lalle ubanmu, haƙĩƙa, yanã cikin ɓata bayyananniya.
9
Ku kashe Yũsufu, kõ kuwa ku jẽfa shi a wata ƙasa, fuskar ubanku ta wõfinta sabõda ku, kuma ku kasance a bãyansa mutãne sãlihai.
10
Wani mai magana daga cikinsu ya ce: "Kada ku kashe Yũsufu. Ku jẽfa shi a cikin duhun rĩjiya, wasu matafiya su tsince shi, idan kun kasance mãsu aikatãwa ne."
11
Suka ce: "Yã bãbanmu! Mẽne ne a gare ka ba ka amince mana ba a kan Yũsufu, alhãlikuwa lalle ne mũ, haƙãƙa mãsu nashĩha muke a gare shi?"
12
Ka bar shi tãre da mu a gõbe, ya ji dãɗi, kuma ya yi wãsa. Kuma lalle ne mu, a gare shi, mãsu tsaro ne.
13
Ya ce: "Lalle ne ni, haƙãƙa yanã ɓãta mini rai ku tafii da shi, Kuma inã tsõron kerkẽci ya cinye shi, alhãli ku kuwa kunã mãsu shagala daga gare shi."
14
Suka ce: "Haƙĩƙa idan kerkẽci ya cinye shi, alhãli kuwa munã dangin jũna, lalle ne mũ, a sa'an nan, hakĩka, mun zama mãsu hasãra."
15
To, a lõkacin da suka tafi da shi, kuma suka yi niyyar su sanya shi a cikin duhun rĩjiya, Muka yi wahayi zuwa gare shi, "Lalle ne, kanã bã su lãbari game da wannan al'amari nãsu, kuma sũ ba su sani ba."
16
Kuma suka je wa ubansu da dare sunã kũka.
17
Suka ce: "Yã bãbanmu! Lalle ne, mun tafi munã tsẽre, kuma muka bar Yusufu a wurin kãyanmu, sai kerkẽci ya cinye shi, kuma kai, bã mai amincẽwa da mu ba ne, kuma kõ dã mun kasance mãsu gaskiya!"_
18
Kuma suka je, a jikin rigarsa akwai wani jinin ƙarya. Ya ce: "Ã'a, zukatanku suka ƙawãta muku wani al'amari. Sai haƙuri mai kyau! Kuma Allah ne wanda ake nẽman taimako (a gunSa) a kan abin da kuke siffantãwa."
19
Kuma wani ãyari ya je, sai suka aika mai nẽman musu rũwa, sai ya zura gugansa, ya ce: "Yã bushãrata! Wannan yãro ne." Kuma suka ɓõye shi yanã abin sayarwa. Kuma Allah ne Masani ga abin da suke aikatãwa.
20
Kuma suka sayar da shi da 'yan kuɗi kaɗan, dirhamõmi ƙidãyayyu, Kuma sun kasance, a wurinsa, daga mãsu isuwa da abu kaɗan.
21
Kuma wanda ya saye shi daga Masar ya ce wa mãtarsa, "Ki girmama mazauninsa, akwai tsammãnin ya amfãne mu, kõ kuwa mu riƙe shi ɗã."Kuma kamar wancan ne Muka tabbatar ga Yũsufu, a cikin ƙasa kuma dõmin Mu sanar da shi daia fassarar lũbũru, kuma Allah ne Marinjãyi a kan al'amarinSa, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba."
22
Kuma a lõkacin da ya isa mafi ƙarfinsa, Muka bã shi hukunci da ilmi. Kuma kamar wancan ne Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
23
Kuma wadda yake a cikin ɗãkinta, ta nẽme shi ga kansa, kuma ta kukkulle ƙõfõfi, kuma ta ce, "Yã rage a gare ka!" ya ce: "Ina neman tsarin Allah! Lalle shĩne Ubangijina. Yã kyautata mazaunina. Lalle ne shĩ, mãsu zãlunci ba su cin nasara!"
24
Kuma lalle ne, tã himmantu da shi. Kuma yã himmantu da ita in bã dõmin ya ga dalĩlin Ubangijinsa ba. Kãmar haka dai, dõmin Mu karkatar da mummũnan aiki da alfãsha daga gare shi. Lalle ne shi, daga bãyinMu zaɓaɓɓu yake.
25
Kuma suka yi tsẽre zuwa ga ƙõfa. Sai ta tsãge rigarsa daga bãya, kuma suka iske mijinta a wurin ƙõfar. Ta ce: "Mẽnene sakamakon wanda ya yi nufin cũta game da iyãlinka? Fãce a ɗaure shi, ko kuwa a yi masa wata azãba mai raɗaɗi."
26
Ya ce: "Ita ce ta nẽme ni a kaina."Kuma wani mai shaida daga mutãnenta ya bãyar da shaida: "Idan rigarsa ta kasance an tsage ta daga gaba, to, tã yi gaskiya, kuma shĩ ne daga maƙaryata."
27
Kuma idan rigarsa ta kasance an tsãge ta daga bãya, to, tã yi ƙarya, kuma shĩ ne daga mãsu gaskiya.
28
Sa'an nan a lõkacin da ya ga rĩgarsa an tsãge ta daga bãya, ya ce: "Lalle ne shi, daga kaidinku ne, mata! Lalle ne kaidinku mai girma ne!"
29
Yusufu! Ka kau da kai daga wannan. Kuma ki nẽmi gãfara dõmin laifinki. Lalle ne ke, kin kasance daga mãsu kuskure.
30
Kuma waɗansu mãtã a cikin Birnin suka ce: "Matar Azĩz tanã nẽman hãdiminta daga kansa! Haƙĩƙa, yã rufe zũciyarta da so. Lalle ne mũ, Munã ganin taa cikin ɓata bayyanãnna."
Sonraki 30 ayet →